Hukumar KUST Tashirya Tsaf Dan Daukar Mataki Mai Tsauri Ga Samarin Da Suka Matsawa Mata Masu Sa Abaya Lamba.

 





Hukumar KUST dai ta ce za ta ɗauki "mummunan mataki" kan ɗaliban da suka ci zarafin ɗalibar.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a ranar Talata, shugaban sashen harkokin ɗalibai ya nemi afuwar ɗalibar sannan ya buƙaci ta shigar da ƙara a hukumance domin neman haƙƙinta.

"Hukumar Kano University of Science and Technology Wudil ta samu ƙorafe-ƙorafe daga shafukan zumunta game da wata ɗaliba da ɗalibai maza suka ci zarafinta saboda ta saka abaya," a cewar sanarwar.

"Ni shugaban sashen harkokin ɗalibai zan ɗauki mummunan mataki a kan wannan lamari. Ɗalibai su sani cewa su ba hukuma ba ce da za su ci zarafi ko ɗaukar mataki kan wani, sai dai kawai su kai rahoto wurin jami'an tsaro."

Sanarwar ta ce abaya ba ta saɓa wa dokar saka tufafi ta jami'ar ba, "saboda haka ɗalibar ba ta karya wata doka ba".